Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-03 15:19:51    
Titin Hefangjie da ke birnin Hangzhou

cri

Bayan da masu yawon shakatawa suka ci abubuwan marmari, to, watakila za su mai da hankulansu kan fasahohin musamman da masu fasahar gargajiya suka nuna. Fasahohin gargajiya masu ban sha'awa su ma suna kasancewa sigar musamman ta titin Hefangjie. Mr. Ji Changyi, wani mai fasahar kera mutum-mutumi da sukari, shekarunsa ya kai 75 da haihuwa. Ko da yake ya riga ya yi ritaya, amma bayan da shugabannin kwamitin harkokin titin Hefangjie suka san cewa, ya gwanance wajen kera mutum-mutumi da sukari, sai sun gayyace shi da ya nuna fasahar musammansa a wannan titi. Game da wannan Mr, Ji ya ce,

'Na yi shekaru 6 ina nuna fasahata a wannan titi. An fara kera mutum-mutumi da sukari tun daga yarantaka. Ina sayar da irin wadannan abubuwan sukari har tsawon shekaru 55. Na iya kera daruruwan abubuwa masu siffofi daban daban. Yara da baligai har ma da mutanen da suka zo daga kasashen waje dukkansu suna sha'awar sayen abubuwan da na kera.'


1 2 3