Bayan da Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, an samu manyan sauye-sauye a kasar a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma da al'adu da dai sauransu.
Kasar Sin ta zamanin yau tana bude kofarta fiye da yadda dimbin jama'a ke tsammani, kuma gwamnatin kasar na gudanarwa a fili kuma cikin inganci fiye da yadda wasu kasashen waje ke tsammani. Yau Sinawa suna da hakuri da kuzari fiye da yadda wasu kasashen waje ke tsamani, kuma hakkinsu na samun karin girmamawa da kariya fiye da da. Duk wadannan sauye-sauye masu kyau sun bayyana sosai a yayin da ake ba da agaji.(Lubabatu) 1 2 3 4
|