Bayan da girgizar kasa ta afka wa gumdumar Wenchuan ta lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin a ran 12 ga watan nan da muke ciki, yadda kasar Sin ta bayar da agaji cikin hanzari da inganci ya sami yabo sosai daga gamayyar kasa da kasa, haka kuma ya kawo wani gefe na daban na kasar Sin a gaban kasashen duniya, wato gwamnatinta da ke gudanar da aikinta cikin inganci da kuma daukar alhakin da ke bisa wuyanta da jama'arta da ke kaunar juna da hada kan juna.
Sa'o'i kalilan ne bayan aukuwar girgizar kasar, sai firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya isa yankunan da girgizar kasar ta auku, sassan kula da harkokin jama'a da sufuri da kiwon lafiya da sadarwa da dai sauransu su ma sun fara aiki da tsarin ko ta kwana cikin hanzari. A cikin rahoton da ta bayar, Madam Barbara Demick, wakiliyar jaridar Los Angeles Times da ke nan birnin Beijing, ta nuna yabo da cewa, gwamnatin kasar Sin ta ba da gudummawa cikin hanzari ga yankunan da girgizar kasar ta shafa, wannan ya sa aka ga "wata sabuwar kasar Sin", kuma "wata kasar Sin mai tausayawa da kuma karfi."
1 2 3 4
|