Yadda kasar Sin ta bayar da labaran girgizar kasar ma ya sami amincewa daga gida da waje. Minti 10 bayan aukuwar girgizar kasar, sai Sin ta bayar da labarinta, kafofin yada labarai na kasar ma sun ba da rahotanni a kan girgizar kasar, har ma gidan telebijin kasar da dai sauran gidajen telebijin na wurare daban daban na kasar sun dakatar da shirye-shiryensu na yau da kullum, sun fara nuna yadda ake ba da agaji kai tsaye.
Jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya ta ce, yadda gwamnatin kasar Sin ta mayar da martani kan aukuwar girgizar kasar cikin hanzari ya cancanci yabo, kuma ko kadan ba ta boye tsananin girgizar kasar ba.
Jama'ar kasar Sin sun nuna himma sosai wajen ba da agaji. Ya zuwa jiya 21 ga wata, yawan kudaden agaji da al'ummar kasar Sin suka bayar ya riga ya wuce kudin Sin yuan biliyan 4. A yayin da gwamnati ke kokarin ba da agaji, dimbin masu aikin sa kai sun kwarara zuwa yankunan da girgizar kasar ta shafa daga wurare daban daban na kasar Sin, don ba da nasu taimako. Jaridar Lianhe Zaobao ta kasar Singapore ta bayar da labarin cewa, girgizar kasa mai tsanani ta girgiza zukatan jama'ar kasar Sin, haka kuma ta fito da kishin kasa nasu.
1 2 3 4
|