Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-26 08:49:40    
Tufafin kabilar Hui

cri

Kabilar Hui tana bin addinin musulunci, wani muhimmin sashe daga zaman rayuwar 'yan kabilar shi ne yin addu'o'i daban daban na addini. An haifi madam Ma Shumin a wani iyali na kabilar Hui, ta zana tufafi ne bisa tushen addininsu. Ta yi la'akari sosai kan abin musamman na kabilarsu a lokacin da take zana tufaffi.

Kabilar Hui ta taho a kasar Sin a cikin farkon karni na 13. A cikin wancan lokaci, 'yan tsakiyar Asiya da Larabawa da kuma 'yan kasar Iran sun zo nan kasar Sin, kuma sun hada da kabilar Han da kabilar Uygur tare, sabo da haka sannu a hankali kabilar Hui ta kafu. Yanzu, 'yan kabilar suna yin zamansu a ko ina a kasar Sin. Ba su da harshe nasu, kuma ba su da harafinsu, suna yin zamansu tare da sauran kabilu. Sabo da haka, tufafin kabilar Hui ba su da tsarin musamman nata, ban da cewar maza su kan sa farar hula, kuma mata su kan sa dan kwali a kansu yayin da suke yin salla, ba su da tufafi na musamman nasu. Kuma wannan dalili ne da ya sa 'yan kabilar Hui da yawa kamar Madam Ma Shumin suke so su bayar da gudummowarsu a wannan fannin. Madam Ma Shumin ta ce,"Ina fatan kabilar Hui tana da tafafin kabilar a wasu muhimman filaye. Sabo da bisa matsayinta na wata kabila, tufafinta wani harshe ne. Amma har zuwa yanzu, tufafin kabilar ba su da yawa sosai, sabo da haka ina jin bakin ciki sosai."


1 2 3