Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 18:21:12    
Sinawa na kara samun wayewar kai a matsayin 'yan kasa

cri

A yunkurin yaki da girgizar kasa kuma, wayewar kai na jama'ar kasar Sin ya fito ne a yayin da suke nuna jimami ga wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa.

Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta yanke wata shawara cewa, kwanaki 3 wato daga ran 19 zuwa ran 21 ga watan Mayu na wannan shekara su zama ranakun yin ta'aziyya na duk kasar Sin. A ran 19 ga wata da yamma da misalin karfe 2 da minti 28, da aka buga jiniya da ke alamanta zuwan jiragen saman yaki na makiya, matafiya sun daina tafiya, ma'aikata sun daina ayyukansu, dukkan jama'ar kasar Sin sun nuna jimami har tsawon mintoci 3 ga wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa. A ran nan da dare kuma, jama'ar larduna da birane da yawa sun kuna wutar kandir, domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa.

A cikin wannan aikin ceto na girgizar kasa, Sinawa sun dauki matakai da kansu, sun bayyana cewa, aikin ceto ba kawai wani nauyi da ke bisa wuyan gwamnati ba, har ma ya zama wani hakkin 'yan kasa, da kuma nauyin da ke bisa wuyansu. A sa'i daya kuma, wannan ya bayyana cewa, tare da bunkasuwar zaman takewar al'umman kasar Sin, Sinawa suna kara samun wayewar kai a matsayin 'yan kasa.(Danladi)


1 2 3