Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 18:21:12    
Sinawa na kara samun wayewar kai a matsayin 'yan kasa

cri

Mr. Chen Yan shi ne shugaba ne na wani kamfanin zaman kansa da ke birnin Dongguan na lardin Guangdong na kasar Sin. A rana ta biyu bayan faruwar girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, Chen Yan da matarsa sun je birnin Mianzhu na lardin Sichuan tare da kayayyakin agaji. A cikin wadannan kwanaki da suka gabata, ya riga ya ceci yara fiye da 20, sakamakon haka ne, Chen Yan ya zama daya daga cikin masu aikin sa kai da suka fi ceton jama'a daga girgizar kasa. Mr. Chen Yan ya ce,

'A da, na taba gudanar da aikin ceto a runduna. Ina tsammani suna da na'urori na fasahohin musamman, tare da kwarewata, da kuma kwarewarsu, za mu iya samun hanyoyi masu kyau wajen kara ceton jama'a.'

A gun ayyukan ceto na babbar girgizar kasa, jama'ar kasar Sin, da kuma kungiyoyin da ba na gwamnati ba sun shiga cikin ayyukan ceto sosai da sosai, sun kara saukewa nauyin da ke bisa wuyansu. Wannan ya bayyana cewa, Sinawa na kara samun wayewar kai a matsayin 'yan kasa.


1 2 3