Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 18:21:12    
Sinawa na kara samun wayewar kai a matsayin 'yan kasa

cri

Wayewar kai a matsayin 'yan kasa irin wayin kai ne na farar hula, sakamakon bunkasuwa da zaman takewar al'umma da ci gabansa.

A hakika dai, tun bayan da kwamitin tsakiya na kungiyar matasa ta kasar Sin ya fara gudanar da ayyukan sa kai na matasa a shekarar 1993 har zuwa yanzu, ra'ayin ba da hidima da sa kai ya kara yaduwa a kasar Sin. An riga an dasa ra'ayin sa kai na 'ba da hidima, da zumunta, da taimakawa juna, da ci gaba' cikin zuriyar jama'a. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, yawan jama'ar da suka taba gudanar da ayyukan sa kai na kasar Sin ya riga ya kai miliyan 80. Aikin ceto na girgizar kasa a gundumar Wenchuan ya zama wani kyakkyawan misali da ya bayyana ra'ayin masu aikin sa kai.

Shahararren mawaki na kasar Sin Mr. Li Shuangjiang ya ce,

'A halin yanzu, iyalammu da yawa, ciki har da wasu yara suna cikin wuraren da suka ruguje sakamakon girgizar kasa. Mene ne za mu iya yi ? Wata dabara kawai ita ce mu ba da taimako bisa iyawarmu, domin mu ceci yaranmu, da mahaifanmu, da iyalanmu daga girgizar kasa tun da wuri.'

Mr. Li Shuangjiang ya yi wannan kira ne a gun wani taron ba da kyautattuka ga yankunan girgizar kasa. A ran 18 ga wata da dare, gidan TV na tsakiya na kasar Sin ya shirya wani taron ba da kyaututtuka da ya fi girma bisa mataki tun bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin, inda aka samu kyautar kudi da yawansu ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 1.5. Muna iya cewa, dukkan jama'ar kasar Sin sun shiga cikin aikin ceto a wannan karo, wannan kuma ya zama wani kyakkyawan abu na aikin ceto.


1 2 3