Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 15:13:10    
Nuna fara'a ya iya yaki da bala'i

cri

Wannan mutumin Amurka mai shekaru 67 da haihuwa ba kawai ya ga abubuwa masu ban tausayi da suka faru a Los Angeles ba, har ma wurin da yake zama wato jihar Massachusetts ya yi suna ne a Amurka saboda shan wahalar mahaukaciyar guguwa. Bala'i daga inadallahi da ya sha gamuwa ya sanya Paul ya san cewa, wajibi ne a nuna fara'a a lokacin da ake fuskantar matsala. Ya ce, taimakon da rukunnoni daban daban na kasar Sin da kuma dukkan kasashen duniya suke bayarwa ya sanya mutanen da ke fama da girgizar kasar su ji dumamar zuciya a zaman rayuwa. Sa'an nan kuma, suna iya samun karfi daga ruhun wasannin Olympic da aikin mika wutar wasannin Olympic ta Beijing yake yadawa. Paul ya ce,'Duniya daya, kuma mafarki daya. In mun kara zurfafa ma'anar wannan jimla, mun iya kara da cewa, mutum daya. Mutanen da suke fama da girgizar kasar a Sichuan ba su fama da girgizar kasar su kadai, dukkan mutanen Sin suna ba su tallafi, mai yiwuwa ne mutane masu tarin yawa ba za su iya gudanar da ayyukan ceto a wuraren da ke fama da girgizar kasar ba, kuma ba za su iya taimakawa wadanda suke fama da girgizar kasar kai tsaye ba, amma mutane suna ba da kayayyakin taimako da kudaden tallafi cikin himma da kwazo. Taimakon da suke bayarwa ta hanyoyi daban daban sun zama abu mai kyau ga lardin Sichuan da kasar Sin, har ma duk duniya gaba daya.'(Tasallah)


1 2 3