Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 15:13:10    
Nuna fara'a ya iya yaki da bala'i

cri

Gregory Brubaker wanda yake aikin koyarwa a jami'ar horar da malamai ta Jiangxi ta kasar Sin ya zo daga Los Angeles ta Amurka. Ya zuwa yanzu, wannan namiji mai shekaru 40 ko fiye ya ji tsoro kadan kan babbarn girgizar kasa da aka samu a garinsa a shekarar 1989. Mr. Brubaker ya bayyana cewa, a yayin da girgizar kasar ta auku, shi ne wani dalibi, abokin arzikinsa ya rasa ransa a cikin wannan mummunar girgizar kasa, sa'an nan kuma, mutane masu yawa sun rasa wuraren kwana a sakamakon bala'in. Amma duk da haka, Mr. Brubaker ya kara da cewa, ko da yake ya zuwan yanzu dai, ya yi kama da ganin abubuwa masu ban tausayi da suka faru a lokacin can, amma girgizar kasa mafi karfi da aka samu a Wenchuan ta Sichuan ta girgiza shi kwarai. Ya ce,'Ya zuwa yanzu na tuna da abubuwan da suka auku a shekarar 1989 sosai, amma girgizar kasar da aka samu a kusa da birnin Chengdu na Sichuan ta fi wadda aka samu a Los Angeles karfi. Na ji an ce, a wata makarantar midil, buraguzen gine-gine sun danne yawancin 'yan makarantar da malamai. Wannan yana da ban tausayi sosai. Amma ina son in gaya wa wadanda suka tsira daga girgizar kasar cewa, girgizar kasar da aka samu a Los Angeles a shekarar 1989 ta kwace rayukan mutane da yawa, ta kuma lalata dimbin gidaje, amma bayan da aka sake gina wannan birni, Los Angeles ta zama wani birnin da ya fi da kyau.'

Mr. Brubaker ya ci gaba da cewa, tabbas ne za a kawar da mummunar inuwar girgizar kasar bayan da aka sake raya wadannan wuraren da ke fama da girgizar kasar. Yana fatan, mutane da suke fama da girgizar kasar za su nuna fara'a kan abubuwan da suke fuskanta a yanzu. Kamar yadda Mr. Brubaker yake gani, Paul Provost, wanda ya zo kasar Sin a shekarar 1999, ya yi shekaru 9 yana aikin koyarwa a jami'ar horar da malamai ta Jiangxi, shi ma yana ganin cewa, a lokacin da wani yake fuskantar bala'i, nuna fara'a ya iya ba da matukar taimako. Ya ce,'Wannan shi ne mummunar girgizar kasa. A lokacin da kake shan wahalhalu, ya kamata ka kara nuna fara'a. Bayan aukuwar girgizar kasar, dukkan mutane sun bai wa wadanda suke fama da girgizar kasar a Sichuan taimako, sun nuna kirki. Bisa wani mataki, wannan shi ne wata dama ga dukkan mutane da su hada kansu.'


1 2 3