Idan hakora suka lalace, su kan yi zafi. Wani sakamakon nazarin da kasar Sweden ta yi ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne zafin hakora wata alamar farko ce ta kamuwa da cutar zuciya. Kuma yiyuwar samun wannan alama ga mata ta kara da kusan kashi 40 bisa dari idan an kwatanta da maza.
Bisa labarin da wata jarida ta kasar Sweden ta bayar a ran 23 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, an ce, manzarta na jami'ar Umea ta kasar sun gudanar da wani bincike ga mutane 186 da suka kamu da cutar zuciya domin su nuna kayayyakin jiki da suka ji zafi kafin barkewar cutar zuciya. Kuma mutane 71 daga cikinsu sun bayyana cewa, sun taba jin zafin hakora, kuma yawancinsu mata ne. Wasu mutane kuma sun taba ganin likita wajen lafiyar hakora kafin barkewar cutar zuciya, amma likitoci ba su gano ainihin dalilin zafin hakora, daga baya kuma an dauke su zuwa sashen kula da cuttuttukan cikin jikin dan Adam, sai a gano cewa, sun kamu da cutar zuciya.
Ban da wannan kuma manazarta sun nuna cewa, bai kamata ba a dauka cewa idan ana jin zafin hakora, wata alama ce ta kamuwa da cutar zuciya. Amma idan ana jin zafin hakora na dukkan gefuna biyu, kuma zafin yana kara tsananta yayin da ake ci abinci, to ya kamata a mai da hankali kuma ya je asibiti domin ganin likita nan da nan.(Kande Gao) 1 2 3
|