Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 16:12:59    
Shan lemo kullum zai iya yin illa ga hakoran dan Adam

cri

A kwanan nan, manazarta na jami'ar south Illinois ta kasar Amurka sun gano cewa, mai yiyuwa ne shan lemo kullum zai iya lalata sinadarin enamel da ke kan hakora.

An bayar da wannan sakamakon nazari ne a kan mujallar ilmin hakora na jama'a ta kasar Amurka. Manazarta na jami'ar sun gudanar da wani gwaji kan yadda lemon kwalba ko na gwangwani ke lalata hakora. Manazarta sun sayi ire-iren lemon sha guda 20 kamar Coka Cola da Pepsi Cola da dai sauransu. Bayan da aka bude su, sai nan da nan aka auna yawan sinadarin acid da ke cikinsu, daga baya kuma an fere enamel daga hakoran da aka cire ba da jimawa ba. Bayan da aka auna nauyinsu, sai aka sanya su a cikin lemon sha, kuma bayan awoyi 48, an fitar da su daga lemon sha don sake auna nauyinsu.

Sakamakon nazarin ya bayyana cewa, yawan nauyin enamel da ke cikin lemon sha iri 7 ya ragu fiye da kashi 5 bisa dari.


1 2 3