Manazarta sun nuna cewa, ko da yake ba za a ajiye lemon sha a cikin baki har kwanaki biyu ba kamar yadda aka yi a cikin gwaji, amma wasu lemon sha suna fara lalata hakora tun lokacin da aka fara shansu, kuma a kwana a tashi, lalacewar hakora za ta kara tsananta.
Ban da wannan kuma samakon nazarin ya nuna cewa, yawan sinadarin acid da ke cikin lemon sha ba sandari daya tak ba ne wajen lalata hakora, lalacewar hakora da lemon sha ke haddasawa yana da nasaba da ire-iren lemon sha da ire-iren sinadarin acid da ke cikin lemon sha da kuma yawan sinadarin calcium da ke cikinsa.
Manazarta sun bayyana cewa, sinadarin acid da ke cikin ko wane irin lemon sha yana iya lalata hakora, shi ya sa ya kamata a yi rigakafi a kansa. Kuma sun ba da shawarar cewa, ya fi kyau a yi amfani da tsinke lokacin da ake shan lemo, ta yadda za a iya rage hadarin da ke tsakanin lemo da hakora. Ban da wannan kuma ya fi kyau a sha lemo lokacin da ake cin abinci.
1 2 3
|