Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 15:28:55    
Kauyen al'adun gargajiya na kasar Sin a birnin Shenzhen

cri

Don kara jawo hankulan karin masu yawon shakatawa da su nuna sha'awa kan al'adun gargajiya na al'ummar kasar Sin, a kan nuna babban wasan kwaikwayo a ko wace rana da dare. Mr. Peng Li ya yi yini daya yana yawo a cikin wannan kauye, amma ba ya so komawa gida, ya yi shirin kallon wannan wasan kwaikwayo tare da masoyiyarsa. Ya ce,

'Yau na kawo wa wannan kauyen al'adun gargajiya ziyara tare da masoyiya saboda ta gaya mini cewa, akwai bukukuwa da yawa a nan, kuma za mu iya dandano abinci mai dadin ci, haka kuma, mun iya kallon wasannin kwaikwayo masu ban sha'awa.'

Baya ga yin amfani da dandamalin zamani, wannan wasan kwaikwayo ya nuna al'adun gargajiya na kananan kabilu da yawa na kasar Sin, kamar kabilar Tujia da kabilar Hui da kabilar Yi. 'Yan wasan da suka nuna wasan kwaikwayon dukkansu sun zo daga babban yankin kasar Sin, kuma su ne 'yan kabilun Uygur da Bai da Zhuang da Tibet. Ma iya cewa, wannan babban wasan kwaikwayo ya hada al'adar kananan kabilu da ta zamani tare, yana da ban sha'awa ainun.(Tasallah)


1 2 3 4