Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 15:28:55    
Kauyen al'adun gargajiya na kasar Sin a birnin Shenzhen

cri

A cikin kauyen al'adun gargajiya na kyakkyawan kasar Sin, a karo na farko ne kasar Sin take nuna fasahohin gargajiya na kabilu daban daban da halayen musamman nasu da kuma gine-gine nasu a cikin wani babban wurin yawon shakatawa na al'adu. An gina kauyuka guda 25 na 'yan kabilu 22 na kasar Sin a ciki. Ta hanyar shirya wasannin kwaikwayo na nuna sigogin muamman na kananan kabilu da nune-nunen fasahar kera kayayyaki da hannu ta gargajiya da shirya bukukuwan gargajiya a lokaci-lokaci ne ake iya nuna tsantsar al'adun gargajiya na kabilu daban daban na kasar Sin daga dukkan fannoni. Mr. Wang ya kara da cewa,

'A gun bikin kallon fitilu na gargajiya na kasar Sin da ya gabata, mun shirya harkar kallon fitilu da gasar kacici-kacici. Masu yawon shakatawa sun iya shiga gasar kacici-kacici, da dare kuma sun iya kallon motocin da aka kayatar da su da fitilu masu launuka daban daban. Wannan harka ta fi samun amincewa daga masu yawon shakatawa. A daren bikin kallon fitilun kawai, mun karbi masu yawon shakatwa fiye da dubu 12. Mun kuma gano cewa, yawan masoya da iyalai ya kai kashi 90 cikin dari bisa na masu yawon shakatawa da suka kawo wa kauyenmu ziyara.'


1 2 3 4