Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 15:28:55    
Kauyen al'adun gargajiya na kasar Sin a birnin Shenzhen

cri

A wannan kauye, ana rarraba kananan mutum-mutuma da dabbobin tangaran fiye da dubu 50 a tsakanin wadannan kananan abubuwa, ta haka ana iya nuna wa masu yawon shakatawa al'adun gargajiya da 'yan kabilu daban daban na kasar Sin suke bi a zaman rayuwarsu da kuma sigogin musamman nasu. A sa'i daya kuma, kauyen al'adun gargajiya na Shenzhen ya hada da fasahar tsara kananan lambuna a cikin tukunyar fure ta gargajiya da fasahar tsara lambuna ta zamani tare, don haka, kauyen ya zama abin koyi a fannin fasahar tsara lambuna irin ta kasar Sin. Sa'an nan kuma, akwai wani yankin musamman da aka kebe a cikin kauyen al'adun gargajiya na Shenzhen domin yada al'adun gargajiya na kasar Sin. Wang Dan, mai kula da kauyen al'adun gargajiya na Shenzhen ya yi karin bayani da cewa,

'Halin musamman na wannan yanki da kuma amfaninsa su ne yada al'adun gargajiya na kasar Sin. Mun hada al'adun gargajiya na kasar Sin da na kabilu daban daban na kasar da zaman rayuwar mutane ta zamanin yau tare. Ta haka, yankin musamman nan yana kasancewa da abun yawon shakatawa mai nuna sigar musamman ta al'adu, wanda kuma ya iya biyan bukatu a fannoni daban daban.'


1 2 3 4