Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 14:38:26    
Mr. Sarkozy ya sami sakamako da yawa daga ziyararsa a Tunisia

cri

Sa'an nan kuma, bangarorin 2 sun daddale yarjeniyoyin tattalin arziki da ciniki da yin hadin gwiwar kimiyya da fasaha da kuma yarjejeniyoyin tsari kan kulla dangantakar abokantaka a harkokin kudi da dai sauransu. Ban da wannan kuma, Tunisia ta yi amfani da kudin Euro fiye da biliyan 2 domin sayen jiragen sama daga kamfanin Airbus ta Faransa. Kazalika kuma, Faransa ta bai wa Tunisia gatanci a fannoni daban daban.

Tunisia ta dora muhimmanci sosai kan ziyarar da Mr. Sarkozy ya kai mata. Shugaba Ben Ali na Tunisia ya raka takwaransa na Faransa da kansa, ya kuma shirya gaggarumin bikin maraba da shi a cibiyar birnin Tunis. Tunisia tana fatan za ta inganta dangantaka a tsakaninta da sauran kasashe mambobin kungiyar EU ta hanyar kyautata dangantaka a tsakaninta da Faransa. Dukkan bangarorin Tunisia da Faransa suna ganin cewa, Mr. Sarkozy ya sami cikakkiyar nasarar ziyarar Tunisia. Tunisia da Faransa sun raya hulda a tsakaninsu zuwa sabon mataki, kuma ziyarar da Mr. Sarkozy ya yi ta aza harsashi wajen kaddamar da shirin kawancen kasashen yankin tekun Bahar Rum a watan Yuli a Paris.(Tasallah)


1 2 3