Amma kasashen da ke gabar kudancin tekun Bahar Rum suna fatan za a inganta dangantakar tattalin arziki da ciniki tare da kungiyar EU ta hanyar kafa wannan kawance, a maimakon koma baya, wato bin umurnin kungiyar EU.
Inganta dangantaka a tsakanin kasarsa da Tunisia, muhimmin abu ne daban da Mr. Sarkozy ya mai da hankali a kai a wannan karo. Faransa ta taba yin mulkin mallaka a Tunisia. Yanzu Faransa ta fi zuba jari a Tunisia, haka kuma, ta zama abokiya mafi girma ga Tunisia a harkokin ciniki. Yawan kudaden da suka samu daga wajen yin ciniki a shekarar 2007 ya kai kudin Euro misalin biliyan 7. Yanzu kamfanoni da masana'antu kusan 1200 na Faransa sun kafa rassansu a Tunisia, kuma sun gudanar da shirye-shirye fiye da 1400 a Tunisia.
A wannan karo, Mr. Sarkozy ya kai wa Tunisia ziyara tare da 'yan masana'antu fiye da 500, sun yi tuntuba da shawarwari tare da rukunoni daban daban na Tunisia. A gun shawarwarin, shugabannin kasashen 2 sun bayyana cewa, suna son kafa dangantakar abokantaka domin moriyar juna a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare.
1 2 3
|