Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 14:38:26    
Mr. Sarkozy ya sami sakamako da yawa daga ziyararsa a Tunisia

cri

A karshen watan da ya gabata, shugaba Nicolas Sarkozy na kasar Faransa ya kai ziyarar aikinsa ga kasar Tunisia har na tsawon kwanaki 3. Wannan ne karo na 2 da ya kai wa Tunisia ziyara a cikin kusan shekara guda bayan da ya zama shugaban Faransa. Sake ziyarar Tunisia ta nuna dangantakar gargajiya ta musammam mai karko da zumunci a tsakanin Faransa da Tunisia. Mr. Sarkozy ya sami manyan sakamako biyu daga ziyararsa.

Kowa ya sani cewa, Faransa za ta zama shugaban Kungiyar Tarayyar Turai wato EU a wannan zagaye a watan Yuli na wannan shekara. Makasudin Mr. Sarkozy na ziyarar Tunisia a wannan karo shi ne rubanya kokari wajen yada shirin kawancen kasashen yankin tekun Bahar Rum da ya gabatar a lokacin da yake neman zama shugaban Faransa, ya nemi samun goyon bayan daga Tunisia, wadda kawa ce ta Faransa, kuma take gabar kudancin tekun Bahar Rumdon yin share fage ga shirya taron koli na wannan kawance a ran 13 ga watan Yuli a birnin Paris.

Bisa labarun da kafofin yada labaru na Tunisia suka bayar, an ce, a gun shawarwari da suka yi, shugabannin kasashen 2 sun dora muhimmanci kan tatttauna shirin kawancen kasashen yankin tekun Bahar Rum, dukkansu sun bayyana burinsu na yin kokari tare wajen sa kaimi kan kaddamar da shirin yadda ya kamata. Manazarta sun yi hasashen cewa, ko da yake yawancin kasashe 16 na yankin tekun Bahar Rum sun yi maraba da kuma nuna goyon baya kan shirin da Mr. Sarkozy ya bayar kan kafa kawancen kasashen yankin tekun Bahar Rum, amma bangarorin kudu da arewa na tekun Bahar Rum ba su tsara makasudin bai daya ba. Faransa da sauran kasashe mambobin kungiyar EU suna fatan za a kafa kawancen siyasa da tattalin arziki da al'adu, wanda zai zama cibiyar da ta hada Turai da Afirka, ta haka kasashen Turai za su shiga Afirka. Ban da wannan kuma, Faransa tana fatan yankin tekun Bahar Rum zai zama wani yankin da dukkan kasashen yankin za su sami narasa tare ta hanyar kafa kawancen kasashen yankin tekun Bahar Rum, don haka za su iya yin takara da kasashen Asiya.


1 2 3