
Mr. Liu ya ci gaba da cewa, a cikin wani wa'adin nan gaba, kasar Sin za ta fuskantar babban aiki na yaki da keta ikon mallakar ilmi da satar fasaha. Ya ce,

'A 'yan kwanakin baya, wasu sun kaurar da layin kera haramtattun wallafe wallafe a ketare, domin ci gaba da sayar da kayayyakin zuwa kasar Sin. A cikin kasar Sin kuma, wasu kamfanoni sun kera kayayyakin keta ikon mallakar ilmi ba bisa doka ba, wasu 'yan kasuwa sun sayar da su a wasu wurare. Wannan ya bayyana cewa, muna fuskantar babban aiki na yaki da keta ikon mallakar ilmi da satar fasaha. Sabo da haka ne, ina fatan hukumomin da abin ya shafa da 'yan sanda, da jama'armu za su bi dokokin shari'a dangane da kare ikon mallakar ilmi, domin kago wani muhalli mai kyau, ta yadda za mu iya ba da sabon taimako wajen inganta kwarewar dukkan al'ummar kasar Sin ta yin kire kire.'(Danladi) 1 2 3
|