Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 17:17:46    
An gudanar da harkar lalata abubuwan keta iko da wadanda suka yi satar fasahar kera faye-faye da kuma haramtattun wallafe wallafe bisa sikeli mafi girma a kasar Sin

cri

A ran 20 ga wata, bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, larduna da jihohin da ke da ikon tafiyar da harkokinsu da kansu, da biranen da gwamnatin tsakiya take shugabanta kai tsaye da yawansu ya kai 31 sun lalata abubuwan keta iko da wadanda suka yi satar fasahar kera faye-faye da kuma haramtattun wallafe wallafe bisa sikeli mafi girma a kasar Sin a lokaci daya. Game da haka, shugaban babbar hukuma mai kula da madaba'a da watsa labarai ta kasar Sin, kuma darektan hukumar kula da ikon mallakar ilmi ta kasar Sin Mr. Liu Binjie ya bayyana cewa,

'Ta wannan babban matakin da muka dauka a yau, muna fatan bayyana wa kasashen duniya cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da kare ikon mallakar ilmi, a tsanake ne, gwamnatin kasar Sin za ta kara yaki da abubuwan keta iko da wadanda suka yi satar fasahar kera faye-faye da kuma haramtattun wallafe wallafe, domin kare kwarewar kasar Sin ta yin kirkire-kirkire cikin cin gashin kai, ta yadda za a taimaka wajen kafa wata kasa mai kire kire.'


1 2 3