Haka kuma mataimakin shugaban hukumar kiyaye muhalli ta birnin Beijing Du Shaozhong ya bayyana cewa, yanzu birnin Beijing yana hadin kai tare da birane na larduna biyar da ke makwabtaka da shi domin daidaita matsalar gurbata muhalli tare. Ta wadannan matakai, tabbas ne ingancin iska na birnin Beijing a lokacin yin gasar wasannin Olympics zai kai ma'aunin kasar Sin da kuma bukatun da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta yi. Kuma ya kara da cewa,
"A gabannin gasar wasannin Olympics da kuma lokacin yin gasar, birnin Beijing da biranen lardunan da ke makwabtaka da shi za su kara daukar tsauraran matakai wajen tabbatar da ingancin iska. Haka kuma bayan gasar, za a ci gaba da aikin kyautata ingancin iska na birnin Beijing domin samar da kyakyawan muhalli ga mazaunan birnin a fannonin aiki da kuma zaman rayuwa."(Kande Gao) 1 2 3
|