Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 17:47:51    
Ana iya ba da tabbaci ga ingancin iska na birnin Beijing a lokacin yin gasar wasannin Olympics

cri

Du Shaozhong, mataimakin shugaban hukumar kiyaye muhalli ta birnin Beijing ya bayyana cewa, bayan shekara ta 1998, birnin Beijing ya riga ya dauki matakai fiye da 200 wajen daidaita matsalolin gurbata muhalli sakamakon kwal da motoci da masana'antu da kuma kura, kuma ya samu sakamako mai kyau a bayyane. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, yanzu yawan abubuwan da abubuwa masu gurbata muhalli suke fitarwa a birnin Beijing ya riga ya kai ma'aunin da aka tsara, yawan kurar da ke cikin iska ya samu raguwa sosai, kuma yawan kwanakin da ke da kyakkyawan ingancin iska a birnin Beijing ya karu daga 100 na shekara ta 1998 zuwa 246 na shekarar da ta gabata.

A waje daya kuma, fararen hula na birnin Beijing sun shirya harkoki da yawa bisa son rai domin kyautata ingancin iska. Alal misali, domin rage abubuwan gurbata muhalli da motoci ke fitarwa, dimbin kungiyoyin Beijing da ba na gwamnati ba sun gabatar da shawarar rage yawan lokacin tuka mota. Kuma shawarar ta samu goyon baya daga mutane dubu darurruwa da ke da motoci na birnin Beijing. Zhou Yuelin na unguwar Chongwen ta birnin yana daya daga cikinsu. Kuma ya bayyana cewa,

"Gasar wasannin Olympics ta yi kusa. Domin samar da wani kyakkyawan muhalli da kuma rage abubuwa masu gurbata muhalli, har kullum ina tsayawa tsayin daka kan rage yawan lokacin tuka mota har yini daya a ko wane wata. A waje daya kuma, yin tafiya da kafa da kuma keke zai ba da taimako ga lafiyar jiki. Shi ya sa na yi kira ga dimbin mutane da su shiga kungiyarmu ta kiyaye muhalli."


1 2 3