Har kullum ingancin iska na birnin Beijing a lokacin yin gasar wasannin Olympics wani batu ne da ke jawo hankulan sassa daban daban, domin ba da tabbaci ga ingancin iska, birnin Beijing ya riga ya dauki matakai a jere wajen daidaita batun. Kuma wani jami'in kiyaye muhalli na birnin Beijing ya ce, kasar Sin tana iya cika alkawarin da ta yi wajen kyautata ingancin iska na birnin Beijing domin samar da wani kyakkyawan muhalli ga 'yan wasa da za su shiga gasar wasannin Olympics. To yanzu ga cikakken bayani.
Son Chun Hua da ta zo daga kasar Korea ta Kudu tana karatu a jami'ar jama'ar kasar Sin yanzu. Kuma ta gaya wa wakilinmu cewa, a cikin shekaru 6 da take birnin Beijing, ta gano kyautatuwar ingacin iska na birnin Beijing bisa idanunta. Kuma ta kara da cewa,
"Yanzu ingancin iska na birnin Beijing ya samu kyautatuwa sosai idan an kwatanta da na lokacin zuwana birnin. Kamar yanzu wato lokacin bazara, yawan kurar da ke cikin iska ya samu raguwa a bayyane. Ban da wannan kuma, mazaunan birnin sun kara fahimtar kiyaye muhallin halittu."
1 2 3
|