Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-16 08:26:28    
Halin wasannin Olympic yana cikin zuciyar Akhwari har abada

cri

A shekarar 1968, aka shirya gasar wasannin Olympic a birnin Mexico na kasar Mexico, a karo na farko ne Tanzaniya ta aika kungiyar wakilai zuwa birnin domin shiga gasa tun bayan da ta samu 'yancin kai, Akhwari daya daga cikinsu ne. Da zarar 'yan wasa daga Tanzaniya suka isa Mexico, sai suka ji banbancin muhallin yanayi sosai, Akhwari ya ce:  "Yanayin Mexico ya kawo mana babban tasiri, birnin Mexico yana kan tudu ne, amma mu kan gudu bisa lebur teku, shi ya sa mun gamu da wahala mai tsanani, har ba mu iya yin numfashi ba."

Lallai tsayin birnin Mexico ya fi tsayin lebur teku da mita 2300, wannan ya alamanta cewa, iskar shaka dake cikin iskar birnin ta ragu bisa kashi 30 cikin dari idan an kwatanta shi da na wurin lebur teku, a sanadiyar haka, yawancin 'yan wasan gudun Marathon ba su gama gasa ba. Akhwari ya ce:  "Yan wasa 63 dake cikin 80 ba su gama gasa ba, amma na gama kodayake na sha wahala mai tsanani. A cikin 'yan wasa wadanda suka gama gasa, na zama na karshe wato na 17. " Kafin wannan kuwa, Akhwari ya taba samu zama na farko na gasar gudun Marathon da aka shirya a cikin dukkan gabashin kasashen Afirka da na kudancin kasashen Afirka. Me ya sa bai zama zakara a gun gasar wasannin Olympic? Akhwari ya gaya mana cewa, yayin da yake gudu, ya fadi kan hanya saboda karancin iskar shaka da kuma sanyi, kafar dama ta ji rauni mai tsanani, amma bai bari ba, sai ya ci gaba. Lokacin da Akhwari ya isa wurin gama gasa, an riga an gama bikin ba da kyauta ga masu cin nasara, yawancin 'yan kallo sun riga sun bar filin wasa, sai Akhwari ya ketare layin wurin gama gasa cikin muryar ihu da tafi na sa kaimi, gaba daya ya shafe awa 4 da minti 30 yana gudu. Ya gaya wa manema labarai da suka tambaye shi cewa, kasarsa ta aika shi wurin nan ba soma gasa ba, sai gama gasa ne. Bayan wannan kuma, Akhwari ya shiga gasar duniya sau tarn yawa kuma ya sami sakamako mai gamsarwa. A shekarar 1983, gwamnatin kasar Tanzaniya ta ba shi mindar "jarumin kasa" saboda babban amfanin da ya bai wa sha'anin wasan motsa jiki na kasar.


1 2 3