Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 16:51:07    
Kimiyya da fasaha na zamani sun taimaka wajen ginawa da gudanar da harkokin filaye da dakunan wasannin Olympics na Beijing

cri

A duk tsawon lokacin da ake gina filaye da dakunan wasannin Olympics na Beijing, ban da kimiyya da fasaha na zamani da ake yin amfani da su, an kuma mai da hankali sosai kan kiyaye muhalli da raga bata makamashi.Alal misali: yawan wutar lantarki da aka yi amfani da su a kowace rana wajen gina wannan muhimmin filin wasannin motsa jiki na kasa ya kai kilo-watts 20,000. Amma yawan kudin wutar lantarki da aka yi tsiminsu sakamakon yin amfani da makamashin da aka samo daga hasken rana. Mamban kwamitin kwararru a fannin tsaron gasar wasannin Olympics ta Beijing Mr. Ma Xin ya furta cewa: ' Bari mu dauki misali kan wani gini mai fadin murabba'in mita dubu goma, , kilo-watss dubu daya ne za a iya samo daga karfin hasken rana. Hakan zai iya biya dukkan bukatun da ake da su na yin amfani da makamashi wajen dumama daki'.

Aminai 'yan Afria, a watan Afrilu na wannan shekara ne za a kammala gina dukkan filaye da dakunan wasannin Olympics. Dakarun yin amfani da kimiyya da fasaha na zamani za su kawo kyakkyawan tsaro da kuma sauki ga wassu jerin gasannin jarrabawa da kuma wasannin Olympics da za a soma gudanar a ran 8 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki. Alal misali: akwai bukatu masu tsanani da ake da su na samun yawan saurin bugawar iska a cikin dakunan wasannin kwallon tebur da na badminton domin kuwa saurin bugawar iska fiye da yadda aka saukaka zai haifar da tsaiko ga gasannin. Saboda haka ne dai, aka yi fasali ta kimiyya ga dakin wasannin motsa jiki na Jami'ar Beijing da na Jami'ar masana'antu ta Beijing da za su karbi bakuncin gasannin wasan kwallon tebur da na badminton, inda aka ajiye na'urorin samar da iska na iyakwandishan a karkashin kujerun 'yan kallo. Wani zakaran wasan kwallon tebur na duniya mai suna Wang Hao daga kasar Sin ya furta cewa, lallai na ji dadi ainun da yin gasa a wannan dakin wasannin motsa jiki.


1 2 3