Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, an rigaya an shiga matakin karshe na kammala gina filaye da dakunan wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008. A yanzu haka dai, an soma yin amfani da akasarin wadannan gine-gine. A lokacin da wakilinmu yake daukar labarai, ya samu labarin cewa, an yi amfani da kimiyya da fasaha na zamani masu tarin yawa a yayin da ake gina filaye da dakunan wasannin Olympics na Beijing da kuma tafiyar da harkokinsu da zummar cimma burin yin tsimin makamashi da samun kyakkyawan tsaro da kuma tabbatar da hasashen gudanar da wasannin Olympics cikin kyakkyawan yanayi.
A cikin filaye da dakunan wasannin Olympics na Beijing, lallai muhimmin filin wasannin motsa jiki ya fi janyo hankulan mutane, inda za a gudanar da bikin budewa da kuma rufe gagarumar gasar. Wannan muhimmin filin wasannin, an gina shi ne da karafa masu nauyin Ton 42,000. Mr.Li Jiulin, jami'in aikin gina filin kuma mataimakin babban manajan wani rukunin gine-gine na Beijing ya fada wa wakilinmu cewa: " Wadannan karafa, kasar Sin ce ta yi nazarin narke su ita kanta. Ya zuwa yanzu dai, karafan na'uin Q460E dukansu sun cimma ma'aunin da aka tsara''.
1 2 3
|