Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-10 15:24:25    
Ko a samu sakamako mai kyau a gun taron koli na farko tsakanin kasar Indiya da Afirka?

cri
 

Ra'ayin bainal jama'a sun yi hasashen cewa, lalle wannan taron koli ya samar da wani dandali ga Indiya da Afirka wajen yin cudanya da hadin gwiwa tsakaninsu, kuma ya biya bukatun bangarorin biyu a fannonin siyasa da tattalin arziki bisa wani matsayi. Taron ya daidaita matsayin Indiya da Afirka a kan wasu al'amuran duniya da kuma sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Ban da wannan kuma taron ya kafa tsarin ganawa tsakanin shugabannin Indiya da Afirka a ko wadannen shekaru uku.

Ko da yake taron ya samar da wani kyakkyawan muhalli ga hadin kan Indiya da Afirka, amma ana bukatar ci gaba da yin bincike kan cewa, ko za a samu sakamako mai kyau cikin sauri ta hanyar hadin kansu ko a'a.

Da farko, kasashen Afirka 14 sun halarci taron, wadanda suka kai kusan rubu'i kawai cikin dukkan kasashe fiye da 50 na nahiyar Afirka. Shugabannin Kasashen Masar da Nijeriya da dai sauran kasashen da suke takawa muhimmiyar rawa a shiyyar Afirka ba su halarci taron ba.


1 2 3