Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-10 15:24:25    
Ko a samu sakamako mai kyau a gun taron koli na farko tsakanin kasar Indiya da Afirka?

cri

A ran 9 ga wata, a birnin New Delhi, babban birnin kasar Indiya, an rufe taron koli na farko na dandalin tattaunawa tsakanin Indiya da Afirka wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa. Ko da yake an zartas da 'sanarwar Delhi' da kuma 'yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Indiya da Afirka' a gun taron, amma manazarta sun nuna cewa, bayan da Indiya da Afirka suka rasa dora muhimmanci ga juna har shekaru fiye da 20, yanzu taron ya samar da wata dama ce kawai wajen yin cudanya tsakaninsu da kuma fahimtar juna, shi ya sa idan bangarorin biyu suna son cimma burinsu na hadin kansu da kuma samun sakamako mai kyau, to za su bi wata doguwar hanya.

Gwamnatin kasar Indiya ita ce ta shirya wannan taron koli na dandalin tattaunawa tsakanin Indiya da Afirka, shugabannin kasashen Afirka 14 da kuma shugaban kwamitin kula da Kungiyar Tarayyar Afirka Alpha Konare sun halarci taron. Shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron sun bayyana cewa, Indiya da Afirka suna da buri iri daya kan gyare-gyaren MDD da dai sauran al'amura, kuma Afirka tana bukatar sakamako mai kyau da kuma fasahohin da Indiya ta samu a fannonin raya fasahar sadarwa da aikin gona da aikin koyarwa. Ban da wannan kuma bangarorin biyu suna mai da hankulansu kan samar da abinci mai inganci da sauye-sauyen yanayi da shawarwari na Doha na kungiyar WTO da dai sauransu. Firayim ministan kasar Indiya Manmohan Singh ya bayyana cewa, kasar Indiya za ta sa hannu cikin bunkasuwar kasashen Afirka cikin yakini domin tallafa wa Afirka a fannonin kire-kire da sadarwa da raya muhimman ayyukan yau da kullum.


1 2 3