Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-09 14:40:44    
Ayyukan share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing ta sami babban yabo daga kwamitin IOC

cri

A lokacin taron, Mr. Verbruggen ya jagoranci mambobi fiye da 20 na kwamitin tsare-tsaren harkokin gasar wasannin Olympic ta karo na 29 su dudduba kauyen wasannin Olympic na gasar wasannin Olympic ta Beijing da za kammala ginawa nan gaba ba da dadewa ba. Dangane da wannan kauyen wasannin Olympic da za a yi amfani da shi a lokacin zafi na wannan shekara, Mr. Felli, mambar kwamitin kula da harkokin gasar wasannin Olympic ta karo na 29 kuma darektan zartaswa mai kula da harkokin gasar wasannin Olympic na kwamitin IOC ya gaya mana cewa,'Kauyen wasannin Olympic na da kyaun gani kwarai, ko wane daki na da kyau sosai. Ina gamsuwa da ko wane daki da ko wane gado da kuma kujeru. Na yi imani da cewa, 'yan wasa za su gamsu da wadannan.'

Taron da aka yi a makon jiya, cikakken zama ne na karshe da kwamitin tsare-tsaren harkokin gasar wasannin Olympic ta karo na 29 da ke karkashin shugaban kwamitin IOC ya shirya. Ya alamantar da cewa, Beijing ta shiga mataki na karshe wajen shirya gasar wasannin Olympic. Irin wannan wa'adi na karshe na da muhimmanci ainun. Mr. Verbruggen ya bayyana cewa, a shekaru da dama da suka wuce, kwamitinsa da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing sun kiyaye kyakkyawar hadin gwiwa a tsakaninsu. A cikin kwanaki 100 ko fiye na karshe kafin a bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, kwamitinsa zai ci gaba da mara wa Beijing baya wajen shirya gasar wasannin Olympic, zai kuma gama kansa da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing domin yin kokari tare wajen shirya gasar wasannin Olympic mai cikakkiyar nasara.(Tasallah)


1 2 3