Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-09 14:40:44    
Ayyukan share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing ta sami babban yabo daga kwamitin IOC

cri
 

A gun cikakken zama a wannan karo, Mr. Verbruggen ya yi wa gwamnatin Sin godiya saboda goyon bayan da take bayarwa wajen shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, ya kuma nuna yabo sosai kan sakamakon da birnin Beijing da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing suka samu wajen shirya gasar. Ya ce,'Mun yi farin ciki mun kiyasta cewa, tabbas ne gasar wasannin Olympic ta Beijing da za a yi a lokacin zafi a wannan shekara za ta sami cikakkiyar nasara. Yanzu kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing yana gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata. Gasar wasannin Olympic da za a yi a watan Agusta na wannan shekara za ta sami matukar nasara, tabbas ne 'yan wasa za su ci garjiyarta.'

Yanzu Beijing yana rubanya kokarinsa wajen aiwatar da jerin matakan yaki da gurbata iska domin tabbatar da ganin yawan kwanakin da ingancin iska ya yi kyau ko fiye zai kai kashi 70 cikin dari bisa na duk shekara. A kwanan baya, hukumar sa ido kan ingancin iska ta duniya ta riga ta yi wa Beijing kimantawa ta fuskar ingancin iska a watan Agusta na wannan shekara. Mr. Verbruggen ya nuna gamsuwa sosai kan sakamakon kimantawar, ya kuma yi imani da cewa, a lokacin da ake kaddamar da gasar wasannin Olympic, ingancin iska zai yi kyau a Beijing, ko kusa 'yan wasa ba za su sami illa ba.

Sa'an nan kuma, game da ci gaban da Beijing ta samu a fannonin gina filaye da dakunan wasa da wadanda abin ya shafa, Mr. Verbruggen ya kuma nuna gamsuwarsa. Ya ce, sun kai wa yawancin filaye da dakunan wasa ziyara, dukkansu na da matukar kyau. Wadannan ingantattun filaye da dakunan wasa za su karfafa gwiwar 'yan wasa da su yi ta samun sabon ci gaba.


1 2 3