A lokacin da ake mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a duk duniya, a makon da ya gabata, kwamitin tsare-tsaren gasar wasannin Olympic ta karo na 29 da ke karkashin shugabancin kwamitin wasannin Olympic na duniya wato IOC ya kira cikakken zama na karo na 10 a nan Beijing. A gun taron manema labaru da aka yi bayan taron, Hein Verbruggen, shugaban kwamitin tsare-tsaren harkokin gasar wasannin Olympic ta karo na 29 da Gilbert Felli, darekatan zartaswa mai kula da harkokin gasar wasannin Olympic na kwamitin IOC da sauran jami'an kwamitin IOC sun nuna babban yabo ga ayyukan share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing.
A makon jiya da ake gudanar da taron na kwanaki 3, jami'an kwamitin tsare-tsaren harkokin gasar wasannin Olympic ta karo na 29 da na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing sun sha yin taruruka domin kara yin mu'amala da kimantawa kan muhalli da bautawa kafofin yada labaru da 'yan kallo da kwamitocin wasannin Olympic na kasa da kasa da na yankuna, da iyalin wasannin Olympic da hadaddiyar kungiyar wani irin wasa ta duniya da kamfannonin ba da taimakon kudi domiin shirya gasar wasannin Olympic da kuma gasar wasannin Olympic ta nakasassu da dai sauransu.
1 2 3
|