A wannan rana, dalibai da Sinawa da ke zama a Faransa sun runtuma zuwa tituna da wasu shahararrun wurare masu ni'ima don kallon wutar wasannin Olympic da ake mikawa. Sun jinjina jajayen tutoci masu taurari biyar na kasar Sin, kuma da babbar murya suka yi kirarin nuna goyon baya cikin Sinanci da Faranci da marhabinku zuwa birnin Beijing da sauransu. Amma sun yi hakuri ba su mayar da martani ga irin wannan kalubalen da 'yan a-ware na Tibet suka yi ba.
A lokacin da aka mika wutar zuwa filin wasa mai suna Charlety, wakiliyarmu ta kai ziyara ga Madam Beatrice Hess, shahararriyar 'yar wasan ninkaya nakasasshiya a kasar Faransa don jinta bakinta, sai ta ce, ta yi alfahiri sosai da zama mai mika wutar wasannin Olympic na Beijing. Tana fatan dukkan mutane zasu nuna girmamawa ga farin ciki da masu mika wutar ke ji. Dalilin da ya sa haka shi ne domin irin taimakon da suka bayar ya yi yawa har fiye da ake tsammani.
Malam Jiang Xiaoyu, mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya bayar da jawabi cewa, "yau a karni na 21, nauyin da ke sauke a wuyanmu da dukkan jama'a masu kishin wasannin Olympic shi ne kiyaye mutuncin wutar wasannin Olympic da manufarsa game da kiyaye zaman lafiya da aminci da kuma ci gaba. Abin da ya kamata mu bayyana shi ne, jama'ar kasar Sin na son hadin kanta da jama'ar kasashe daban daban don yin kokari tare wajen raya duniya mai jituwa da wadata da zaman lafiya mai dorewa. (Halilu) 1 2 3
|