Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 16:54:32    
An kammala aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Paris

cri

Brinin Paris wuri ne da aka haifi Malam Coubertin. Wannan wani dalilin ne da aka zabi birnin da ya zama wurin da ake mika wutar wasannin Olympic a wannan gami. Haka kuma Husumiyar karfe mai suna Eiffel inda aka fara mika wutar yana daf da wurin da aka haifi Coubertin. Masu yawon shakatawa da yawa na kasashen waje da mazaunan birnin Paris sun taru a gindin husumiyar a wannan rana don kallon bikin mika wutar. Wani namijin kasar Faransa da matarsa wadanda suke tare da 'ya'yansu sun bayyana wa wakiliyarmu cewa, "nan ni'imataccen wuri ne. Ga husumiyar karfen ke haskakawa. Harkar mika wutar wasannin Olympic tana da kyau kwarai."

Amma wasu 'yan a-ware na Tibet sun kulla makarkashiya don neman lalata harkar. Kiri da muzu sun kai farmaki kan wutar wasannin Olympic da masu mika ta. Jin jing, 'yar wasa nakasasshiya wadda ta fito daga kasar Sin ta kammala aikin mika wutar a kan keken nakasassu. A lokacin da take mika wutar ga wani mai mika wutar, ta gamu da farmakin da 'yan a-ware suka kai mata. Tafintarta Malam Han Bing wanda ke cikin motar ba da hidima ya ganam ma idonsa da dukkan abubuwan da suka faru a lokacin. Ya ce, "wasu 'yan a-ware na Tibet sun zabura sun nemi kwace fitalar wutar daga hannun Jin Jing, sun kai mata farmaki a wasu sassan jikinta, allal misali sun ja gashinta da tufafinta da kuma hannayenta da sauransu."


1 2 3