Jiya Litinin, a zango na biyar ne aka mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Paris, hedkwatar kasar Faransa. Ko da yake yayin da ake mika wutar, an gamu da farmakin da 'yan a-ware na Tibet suka kai, amma duk da haka a cikin amon goyon baya da Sinawan da ke zama a kasar Faransa da aminamu masu nuna adalci na kasar suka yi, an mika wutar zuwa filin wasan motsa jiki mai suna Charlety wato wurin karshe a kasar lami lafiya. Yanzu za mu kawo muku labarin da wakiliyar gidan rediyon kasar Sin Deng Yingping ta aiko mana daga birnin Paris.
Da karfe 5 da rabi na maraicen jiya Agogon Paris, mai mika wutar na karshe a Paris ya gudu zuwa filin wasan motsa jiki na Charlety. Cikin amon ganguna, mai mika wutar ya hau kan dakalin shugaba, ya kunna wutar tasar, nan take jama'a suka yi tafi raf-raf-raf. Bayan haka Malam Jiang Xiaoyu, babban jagoran tawagar mika wutar wasannin Olympic na Beijing kuma mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya bayar da jawabi cewa, "yau mun daga wutar wasannin Olympic sama sama a birnin Paris, makasudinmu shi ne domin yadada manufar Olympic da nuna kaunar da 'yan wasannin kasar Sin da jama'arta ke yi wa wasannin Olympic, da nuna girmamawa ga Malam Pierre de Coubertin, uban wasannin Olympic na zamanin yau da tunaninsa. "
1 2 3
|