Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 15:24:36    
Babban tsaunin Qutaishan, dakin nune-nunen gine-ginen gargajiya

cri

Baya ga gine-ginen katako, akwai haikali da yawa a babban tsaunin Wutaishan. Bisa fasahohin gargajiya na kasar Sin ne aka gina irin wannan gine-ginen da ke da baranda mai tsayi, kuma sun bullo a kasar Indiya ta da, ta haka an sami haikali irin na kasar Sin, kuma kasar Sin ta sami sabon irin gine-gine. Haikali da aka samu a babban tsaunin Wutaishan sun hada da na biriki da na duwatsu da na katako da na karfe da na tagulla da na azurfa da dai sauransu. Manya daga cikinsu tsayinsu ya kai mita 50 zuwa mita 60, kanana kuwa tsayinsu ya kai santimita 5. A cikin dukkan haikali a babban tsaunin Wutaishan, babbar hasumiya mai launin fari da ke cikin gidan ibada na Tayuansi ya fi yin suna.

A takaice dai, gine-ginen gargajiya da ke cikin gidajen ibada a babban tsaunin Wutaishan sun iya fadakar da mutane ilmomin gine-ginen gargajiya daga dukkan fannoni, haka kuma, suna kasancewar dakin nune-nunen gine-ginen gargajiya da ke kunshe da gine-ginen gargajiya iri iri, shi ya sa suna da daraja a matsayin bayanan tarihi da kayayyakin fasaha da kuma kayayyakin tarihi.(Tasallah)


1 2 3