Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 15:24:36    
Babban tsaunin Qutaishan, dakin nune-nunen gine-ginen gargajiya

cri

A gun biki na karo na 4 da aka yi a shekarar bara kan al'adun addinin Buddha na babban tsaunin Wutaishan, nagartacciyar fasahar gine-ginen gargajiya da aka samu a babban tsaunin Wutaishan ta sami matukar yabo daga kwararru da masana.

Gine-ginen da aka samu a gidajen ibada a babban tsaunin Wutaishan na da kyaun gani sosai, sun iya bayyana tarihin kasar Sin a jere, haka kuma sun iya nuna siggogin musamman na ko wace daular zamanin da ta kasar Sin. Suna da girma, amma suna hada da kananan bangarori iri iri. An gina su ne a tsanake. Ma iya cewa, su ne gine-ginen gargajiya da aka fi adana su kamar yadda ya kamata a duk kasar Sin.

Yanzu akwai gidajen ibada 68 da aka adana su cikakku, kuma suna da takardun izinin gudanar da harkokin addibin Buddha, a babban tsaunin Wutaishan. Yawancinsu suna cikin yankin da aka fi samun yawan gidajen ibada a garin Taihuai.


1 2 3