
A babban tsaunin Wutaishan, ana iya ganin gine-gine guda 2 kawai a kasar Sin, wadanda aka gina su da katako a zamanin daular Tang, wato shekarar 618 zuwa ta 907 bayan haihuwar Annabi Isa A. S., wato gidan ibada na Foguangsi da kuma gidan ibada na Nanchansi. Babban zauren Dafodian da ke cikin gidan ibada na Nanchansi, gini ne mafi tsoho a kasar Sin wanda aka gina da katako a zamanin daular Tang, kuma har yanzu ana iya ganinsa a kasar Sin, shi ne kuma mai wakilcin gine-ginen da aka gina da katako a zamanin daular Tang na kasar Sin.
Bayan zamanin daular Tang, a zamanin daular Song da ta Yuan da ta Ming da ta Qing, har zuwa farkon shekaru 1900, an gina dimbin manyan gine-gine da katako a babban tsaunin Wutaishan. An gina manyan gine-ginen iri daban daban, wadanda kuma suke sha bamban da juna sosai. Ta haka ana iya ganin wani babban kyakkyawan zane game da gine-ginen zamanin da na kasar Sin a babban tsaunin Wutaishan.
1 2 3
|