A lokacin da manema labaru suka tambaye shi game da wasu tsirarrun mutane sun gabatar da cewa, za su hana shiga wasannin Olimpic, ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun nan fiye da goma da suka wuce, kasar Sin tana aiwatar da manufar yin gayre-gyare da bude wa kasashen waje kofa, kuma ta yi shawarwarin da duniya cikin himma da kwazo, shirya wasannin Olimpic shi ne sakamakon da aka samu bisa manufar nan, yana tsayawa tsayin daka ya nuna adawa da aikin da aka yi ba tare da ba da amfani ga hada kan jama'ar kasashen duniya da shimfida zaman lafiya ba. Ya ce, ya kamata muna ganin hanyar da kasar Sin ta zabi ta yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa kafin shekaru gomai da suka wuce, kasar Sin ta shiga cikin kungiyar WTO, ta shirya wasannin Olimpic, kuma birnin Shanghai zai shirya nune-nunen baje koli na duniya, wadannan su ne sakamakon da aka samu bayan aiwatar da manufar bude wa kasashen waje kofa, bai kamata ba kasar Faransa ta mai da martani ga manufar kasar Sin ta bude wa kasashen waje kofa ta hanyar daukar halin rufe kofa , saboda haka ban yarda da abin da wasu mutane suka fada da cewar wai nuna adawa ga wasannin Olimpic , kowace kasa tana da banbanci da sauran kasashe, ya kamata muna ganin sosai cewa, jama'ar kasar Sin su ne aminan jama'ar kasar Faransa na yau da kullum.
Mr Raffarin ya bayyana cewa, zai shiga wasannin Olimpic na Beijing bisa matsayin wakilin musamman, shi kuma zai dudduba yadda za a yi amfani da harshen Faransanci a lokacin da ake aiwatar da harkokin wasannin Olimpic na Beijing.(Halima) 1 2 3
|