Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 20:29:57    
Wasannin Olimpic na birnin Beijing zai zama kasaitattun wasannin motsa jiki na duk duniya, In ji tsohon firayim ministan kasar Faransa

cri

Ranar 7 ga watan Afril, za a soma mika wutar yolar wasannin Olimpic na Beijing a wurin dake gindin haikalin karfe na Eiffel wanda gini ne da ke iya alamanta birnin Paris. Tsohon firayim ministan kasar Faransa kuma dan majalisar kasar Mr Jean Pierre Raffarin musamman ne ya zabi wurin da ke gindin Eiffel tower don karbi ziyarar da wasu manema labaru na kasar Sin suka yi masa. A lokacin ziyarar, da farko Mr Raffarin ya gaya wa manema labaru cewa, ya yi farin ciki da ganin wasannin Olimpic da za a shirya a birnin Beijing. Ya bayyana cewa, kodayake birnin Paris bai sami damar shirya wasannin Olimpic na shekarar 2012 ba, amma na yi farin ciki da ganin wasannin Olimpic da za a shirya a kasar Sin. Dukkan kasashen duniya suna da ikon shirya wasannin Olimpic, jama'ar kasar Sin su ma suna da ikon shirya wasannin Olimpic, Wasannin Olimpic na Beijing na shekarar 2008 zai zama kasaitattun wasannin motsa jiki na samarin kasar Sin da na duk duniya. Shirya wasannin Olimpic shi ma ya bayyana manufar kasar Sin ta bude wa kasashen waje kofa, a sa'i daya kuma, ya bayyana ma'anar yada halin wasannin Olimpic a ko'ina .

Ya bayyana cewa, ya yi fatan 'yan wasan kasar Faransa za su kara samun lambobin yabo a wasannin Olimpic na Beijing fiye da na da.


1 2 3