Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 20:29:57    
Wasannin Olimpic na birnin Beijing zai zama kasaitattun wasannin motsa jiki na duk duniya, In ji tsohon firayim ministan kasar Faransa

cri
 

Da akwai manema labaru suka tambaye shi cewa, ina ra'ayinsa a kan aikin mika wutar yola ta wasannin Olimpic a birnin Paris, ya bayyana cewa, wutar yola alama ce ta bayyana halin wasannin Olimpic, kuma ta wakilci karfin rayuwa da fatan samari, ta bayyana halin wasannin motsa jiki da tunanin wasannin Olimpic. Bafaransa kuma mahaifin wasannin Olimpic na zamanin yau mai suna Pierre de Coubertin ya taba bayyana cewa, halin wasannin Olimpic shi ne shiga ciki, shiga ciki ya fi samun lambobin yabo muhimmanci, jama'ar da suka zo daga kasashe daban daban na duniya suna begen taruwa gu daya, wasannin Olimpic su ma sun samar musu dama mai kyau, ya kamata kasashe daban daban su girmama wa juna, wannan ne halin wasannin Olimpic ya gabatar da shi. Ya bayyana cewa, A ganina, bai kamata ba a mayar da wasannin motsa jiki bisa matsayin siyasa, ya kamata kasashe daban daban su daidaita manufofinsu bisa halayen musamman da suke kasancewa, bai kamata ba kowace kasa ta yi shishigi a cikin harkokin sauran kasashe. Kasa da kasa su iya tattaunawa bisa zaman daidai wa daida, kasar Faransa ita ma ta yi tattaunawa da kasar Sin da kuma kulla huldar abokantaka da ita bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni.


1 2 3