Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-07 14:00:01    
Bari dimbin mutanen Zimbabwei sun fahimci al'adun kasar Sin

cri
 

Mr. Maxili ya kara da cewa, ko da yake an kafa kwalejin Confucius a jami'ar Zimbabwei shekara 1 kadai, amma ta samu sakamako sosai. A cikin wannan shekarar da ta gabata, mutane 241, ciki har da matan shugaba Robert Mugabe da yaransu biyu sun shiga kwalejin Confucius domin koyon harshen Sinanci. A watan Yuli na shekarar da ta gabata, dalibai 19 na wannan kwalejin sun samu izinin zuwa kasar Sin domin halartar bikin musayar al'adu na mako daya domin sa musu kaimi wajen koyon harshen Sinanci da fahimtar al'adun kasar Sin. A waje daya kuma, a watan Satumba na shekarar da ta gabata, wadanda suka gama karatun koyon harshen Sinanci da kos na al'adun kasar Sin sun samu digiri na farko na jami'ar Zimbabwei. Yanzu galibin mutanen da ke halartar kos na kwalejin Confucius ta jami'ar Zimbabwei 'yan kasuwa da manema labaru ne.

Mr. Maxili ya kara da cewa, shi da abokan hadin guiwa sun riga tsara gajere da tsawon shirin raya kwalejin Confucius a jami'ar. Tun daga watan Agusta zuwa watan Satumba na shekarar da muke ciki, kwalejin Confucius za ta yi amfani da lokacin hutu na jami'ar Zimbabwei domin bude kos na koyon harshen Sinanci ga daliban makarantun firamare.

Mr. Maxili ya jaddada cewa, burin da kwalejin Confucius ta jami'ar Zimbabwei take neman cimmawa cikin dogon lokaci mai zuwa shi ne bude kos a kwalejojin horar da malamai na kasar Zimbabwei, sabo da haka, za a iya horar da wasu malamai wadanda za su iya harshen Sinanci. Daga karshe dai, za a iya koyar da harshen Sinanci tun daga makarantun firamare.


1 2 3