
Ran 16 ga watan Maris na shekarar da muke ciki, rana ce ta cikon shekara 1 da kafuwar kwalejin Confucius ta kasar Zimbabwei. A ran 14 ga watan Afrilu da muke ciki, Mr. Ji Baocheng, shugaban jami'ar jama'ar Sin zai shugabanci wata kungiyar wakilai domin yin rangadin aiki a kwalejin Confucius ta Zimbabwei, kuma zai bayar da jawabi mai take "Abubuwan da kasar Zimbabwei za ta iya koyo daga cigaban tattalin arziki da kasar Sin ta samu".
Mr. Maxili ya ce, "manufar sa ido kan gabashin duniyarmu" da gwamnatin kasar Zimbabwei take dauka ta sa kaimi wajen cigaban huldar da ke tsakanin kasashen Zimbabwei da Sin da cinikayyar da ake yi a tsakaninsu. Sabo da haka, yawan hukumomi da kamfanoni da mutane wadanda suke son fahimtar harshen Sinanci da al'adun kasar Sin da Sinawa yana ta karuwa. Bugu da kari kuma, huldar tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin Sin da Zimbabwei ta samu cigaba cikin sauri.
1 2 3
|