A kwanan baya, lokacin da yake ganawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin, Pecise Maxili, shugaban sashen Zimbabwei na kwalejin Confucius, kuma shugaban kwalejin adabi ta jami'ar Zimbabwei ya ce, "ina fatan dimbin mutanen Zimbabwei za su iya fahimtar kwalejin Confucius, kuma yawan mutanen da ke koyon harshen Sinanci, kuma ke fahimtar al'adun kasar Sin zai samu karuwa."
Mr. Maxili ya ce, za a nuna wa jama'ar Zimbabwei al'adun kasar Sin a lokacin da Mr. Ji Baocheng, shugaban jami'ar jama'ar Sin ya kai ziyara a jami'ar Zimbabwei domin taya murnar cikon shekara 1 da kafuwar kwalejin Confucius a jami'ar Zimbabwei. A waje daya, za a shirya lacca iri iri da suke da nasaba da al'adu da tarihi da manufofin diplomasiyya da kasar Sin ke dauka da addini da abinci masu kamshi da magungunan gargajiya na kasar Sin a cikin kwalejin. Bugu da kari kuma, za a shirya gasar yin jawabi cikin harshen Sinanci. Mr. Maxili ya nuna daruruwan rigunan T-shirt da aka ajiye su a cikin ofishinsa cewa, dukkan ma'aikata da dalibai na kwalejin za su sanya wadannan rigunan T-shirt a lokacin da suke halartar bikin murna.
1 2 3
|