Domin yin la'akari da bukatun 'yan kallo na yankin Amurka ta Arewa, za a aiwatar da tsarin gasanni na musamman a game da gasannin iyo na wasannin Olympics na Beijing,wanda ya sha bamban da yadda aka gudanar a da, wato ke nan za a gudanar gasar fid da gwani ne da dare, agogon wurin na Beijing; amma za a gudanar da gasannin karshe ne da safe, agogon wurin na Beijing. Idan an duba wannan lamari daga fannin ilmin wasannin motsa jiki, to ana iya cewa hakan zai yi illa ga 'yan wasa, wadanda suka saba yin gasar karshe da dare. A gun wannan gasar da aka gudanar, an kuma aiwatar da tsarin gasanni na wasan iyo na gasar wasannin Olympics na Beijing. Hakan ya samar wa 'yan wasa da suka shiga gasar din wata kyakkyawar dama ta saba da bin sabon tsarin gasanni kafin a gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing.
A gun gasar karshe ta wasan iyo cikin 'yanci wato Iyon Free Style na nisan mita 200 na maza da aka gudanar, dan wasa mai suna Paul Biedermann daga kasar jamus ya zama zakara. Amma wannan maki ya yi baya da kimanin dakika shida bisa matsayin bajintar duniya. Bayan gasar, ya furta cewa: " Lallai ajandar wasannin kamar haka da aka yi amfani da ita ta sha bamban da yadda aka yi a da. Saboda haka ne dai, na gamsu da samun wannan kyakkyawan maki. Na yi imanin cewa zan saba da yin gasa da safe a lokacin wasannin Olympics na Beijing".
1 2 3
|