Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-28 12:39:32    
An gudanar da gasar fid da gwani ta wasan iyo na wasannin Olympics na Beijing tare da nasara a cibiyar wasan iyo da ake kira ' Water Cubes'

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, an kawo karshen budaddiyar gasa ta wasan iyo ta kasar Sin a matsayin taken dake cewa "Beijing na yin sa'a", wadda aka shafe kwanaki shida ana yinta a nan birnin Beijing. Gasar nan, gasa ce da aka gudanar a karo na farko tun bayan da aka kammala gina cibiyar wasan iyo mai siffar tafkin wanka ko "Water Cubes" ta kasar Sin, wadda ta kasance wani muhimmin dakin yin gasannin Olympics na Beijing; haka kuma wata muhimmiyar gasa ce ta jarrabawa da aka gudanar domin gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ajandar gasar iyo da aka shirya a wannan gami ta yi daidai da ta gasar iyo ta wasannin Olympics ta Beijing. Ta wanann gasar jarrabawa ne, bangori daban-daban suka buga babban take ga na'u'rorin cibiyar " Water Cubes" da kuma kwarewar da ake da ita wajen gudanar da harkokin cibiyar din.

Ko da yake " Budaddiyar gasar iyo ta kasar Sin" da aka gudanar, wata gasar jarrabawa ce kawai, amma duk da haka, ta sami halarar 'yan wasa sama da 200 daga kasashe da yankuna 29 na duniya, wadanda suka yi yabo sosai ga kyakkyawar fuska ta wannan gini da kuma ingantattun na'u'o'in dake cikin ginin. Mista David Nill dan jarida na kamfanin watsa labarai na kasar Amurka wato NBC ya fada wa wakilinmu cewa: " Wasan iyo, wani irin wasa ne da mutane ke sha'awar yinsa. Mu Amerikawa sun fi son irin wannan wasa. Cibiyar " Water Cubes", wani dakin wasan iyo ne mai kayatarwa. Na taba daukar labarai kan wasannin Olympic da aka gudanar har sau takwas. Lallai wannan cibiyar wasan iyo ta fi sauran dakunan wasan iyo kyaun gani, wadanda na taba ganinsu a da. Ko shakka babu, hotunan da aka dauka ta telebijin daga wannan cibiya za su burge 'yan kallo na dukkan fadin duniya".


1 2 3