Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 15:21:07    
Har ila yau makomar babban zaben kasar Zimbabwe ba ta tabbatu ba tukuna

cri
 

Har ila yau Mr. Mugabe mai shekaru 84 da haihuwa shi ne mafi karfi daga cikin dukkan 'yan takara wajen zaben, tun da aka samu 'yancin al'ummar Zimbabwe a shekarar 1980 zuwa yanzu, ya kasance kan mukamin shugaban kasar, kuma yana daya daga cikin shugabannin da suka fi dadewa a kan karagar mulkin kasashen Afirka.

Mr. Makoni, dan takara mai zaman kansa, kuma tsohon ministan kudi da tattalin arziki shi ne dan takara wajen zaben wanda aka fi sa ran alheri gare shi, shi ne wani babban dan jam'iyyar ZANU-PF, ko da yake an sallame shi daga cikin jam'iyyar, amma har ila yau ya samu magoyan baya da yawa daga cikin jam'iyyar, ban da wannan kuma wani rukunin jam'iyyar adawa wato jam'iyyar MDC shi ma yana nuna goyon bayansa gare shi.

Mr. Tsvangirai, shugaban jam'iyyar adawa wato jam'iyyar MDC ya taba shelar bar shiga yakin neman zabe na wannan karo, amma bayan Mr. Makoni ya sanar da shiga takarar zaben, shi ma ya yi kokarin shiga zaben. (Umaru)


1 2 3