Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 15:21:07    
Har ila yau makomar babban zaben kasar Zimbabwe ba ta tabbatu ba tukuna

cri

A ran 29 ga wata, za a zabi shugaban kasa da majalisar dokoki da kananan hukumomi a kasar Zimbabwe da ke kudancin Afirka. Za a yi wannan babban zabe ne a albarkacin kasar Zimbabwe ta gamu da lalacewar tattalin arziki cikin 7 a jere, kuma ta sha takunkumin da kasashen yamma suka yi mata cikin shekaru da yawa, sakamakon zaben zai jawo babban tasiri ga al'amuran da ake ciki a kasar kuma ga hanyar da za ta bi a nan gaba.

Kwamitin zabe na Zimbabwe ya bayyana cewa, yawan mutanen da suka yi rajista domin shiga babban zabe na ran 29 ga wata ya kai miliyan 5.6, kuma an kafa tashoshin kada kuri'a 9000 a wurare daban-daban na kasar. Yanzu 'yan kallon babban zabe da suka zo daga tarayyar kasashen kudancin Afirka da na sauran kasashe fiye da 40 bisa gayyatar da aka yi musu sun riga sun kama gurabunsu, an riga an share fage sosai domin babban zaben.


1 2 3