Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 15:21:07    
Har ila yau makomar babban zaben kasar Zimbabwe ba ta tabbatu ba tukuna

cri

Bisa ga wani fanni ana iya cewa, wannan babban zabe zai tabbatar da hanyar da Zimbabwe za ta bi a nan gaba, a sa'i daya kuma zai kawo karfin zuciya ga jama'ar Zimbabwe wadanda ke fama da talauci ta yadda za su kyautata zaman rayuwarsu. A watan Disamba na shekarar da ta wuce, Jam'iyyar da ke rike da mulkin kasar da ake kira ZANU-PF ta kira babban taron wakilai na musamman, inda ta zabi Mr. Robert Mugabe, shugaban da ke karagar mulki da ya zama dan takara daya tak na duk jam'iyyar wajen zaben, wanda zai shiga yakin neman zaben shugaban kasa a karo na 6, kuma zai ci gaba da zama shugaban kasar. A ran 5 ga watan Fabrairu na wannan shekara, ba zato ba tsammani Mr. Simba Makoni, mamba na da na ofishin siyasa na jam'iyyar da ke rike da mulki, kuma dan majalisar dokokin kasar, kuma tsohon ministan kudi da tattalin arziki ya yi shelar shiga yakin neman zaben shugaban kasa, kuma cikin gajeren lokaci kadan ya samu goyon baya daga mutanen sassa daban-daban da ke cikin jam'iyyar ZANU-PF da na waje da ita, kuma ya sami iznin shiga takarar zaben bisa matsayinsa na dan takara mai zaman kansa.

Daga cikin 'yan takara 4 da suka samu iznin shiga yakin neman zaben zama shugaban kasar Zimbabwe a wannan karo, ban da Mugabe da Makoni, kuma da akwai Mr. Morgan Tsvangirai, shugaban jam'iyyar adawa wato jam'iyyar MDC. Bisa sakamakon da aka samu wajen binciken ra'ayoyin jama'a an ce, wadannan 'yan takara wajen zabe 3 sun yi kunnen doki wajen yawan goyon bayan da suka samu daga jama'a, kowanensu da yiwuwar zaman shugaban kasa, sabo da haka babban da za a yi a wannan karo a Zimbabwe zai zama yakin neman zabe mafi tsanani cikin tarihin kasar.


1 2 3