Tun daga ranar da aka fara halittar dan adam a duniya, sai aka samu nakasassu. A kasashe dabam daban, nakasassu sun yi yawa daga wajen yawan mutanensu, wato su ne manyan rukunoni da ke cikin kasashen duniya. Saboda haka, matsalar nakassasu matsala ce da ba a iya yin biris da ita ba. Yadda aka daidaita matsalar nakassasu yana daya daga cikin alamun ci gaban da wata kasa ko shiyya ta samu wajen wayin kai. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin da zamantakewar al'umma sun mai da hankulansu sosai da sosai ga sha'anin nakassasu, kuma an sami babban ci gaba wajen bincike da samar wa nakasasu kayayyakin da suke amfani da su na musamman.
A watan Satumba na shekarar 2003, an yi bikin baje kolin kayayyakin da tsofaffi da nakasassu suke yin amfani da su musamman a birnin Nanjing na lardin Jiangsu na kasar Sin, shahararrun masana'antu fiye da 80 da suka zo daga kasashen Holand da Japan da Denmark da Jamus da lardin Taiwan na kasar Sin da sauran kasashe da jihohi guda 6 sun je taron, saboda haka taron nan ya jawo sha'awar hukumomi da tashoshi da gidajen kula da harkokin nakasassu da tsofaffi marasa gata da cibiyoyin warkar da nakasassu na duk kasar Sin don yin musanyar fasahohi da shawarwari da yin kwangilar kayayyakin musamman domin biyan bukatun nakasassu . Ina dalilin da ya sa haka ? Mai kula da harkokin bikin bajen kolin nan malam Wu Yu Zhong ya gaya wa wakiliyarmu cewa, a gun bikin bajen kolin nan, an nuna kayayyaki iri iri fiye da 600 da suka jibinci zaman rayuwar nakasassu da motsa jikinsu da warkar da su da kara lafiyar jikinsu da gine-gine masu ba da taimakon saukin tafiya gare su. Kai daga dukkan fannoni ne aka yada sababbin fasahohi na zamani sosai da sababbin kayayyaki ga nakasassu, wannan ya samar wa ma'aikatun kera kayayyakin nakasassu da wadanda suke amfani da kayayyakin dama mai kyau sosai wajen musanyar fasahohi da sauransu, sa'anan kuma ya ba da amfani mai yakini ga kara yalwata sha'anin nakasassu wajen ci gaban kera kayayyakin nakasassu bisa tsarin kimiyya da ka'idoji da tsarin sana'o'I .
1 2 3
|